Skip to main content

Tushen Magana:

A ranar Asabar, 2 ga watan Mayun shekara ta 2020, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Da Cigaba sun gano wani bidiyo dake nuna dandazon jama’a yayin jana’izar Marigayi Mai  Martaba Sarkin Rano, Alhaji Tafida Abubakar Ila.

Acikin bidiyon wadda aka yadashi sosai a shafin Twitter and manhajar WhatsApp anga yadda cincirundon jama’a keta turmutsitsi cikin nuna juyayi game da rasuwar Sarkin. Hakanan anga yadda mutane sukayi watsi da umarnin bada tazara cudanya dan kare kansu daga cutar Corona.

Tun barkewar cutar Corona, masu yada labaran karya sunyi ta anfani da mutuwar dake aikuwa a Jahar Kano dan yada labaran bogi da nufin dora mutane akan gurguwar fahimta.

Gaskiyar Magana:

Masu tantance sahihancin labarai na CDD, sun gano cewa bidiyon da akace andauke shi ne a lokacin jana’izar Marigayi Martaba Sarkin Ranon andukeshi ne a lokacin binne babban Malami, wato Malam Goni Kolo wanda shima ya rasu ranar da Sarkin Ranon ya rasu.

Marigayi Malam Goni ya rasu ne unguwar Mafoni dake garin Maiduguri yayin da Dr. Tafida Abubakar Ila ya rasu a garin Rano dake Jahar Kano.

Binciken kwakwaf da CDD ta gudanar ya gano cewa yaren Kanuri wanda shine yaren mutanen Maiduguri shine akeyi acikin bidiyon. Yaren da akeyi a Rano sune Fulatanci da Hausa.

Kammalawa: Bidiyon da aka yada a shafin Twitter da WhatsApp dama sauran shafukan sada zumunta na zamani dake nuna dandazon jama’a suna gogayya da juna bidiyo ne da aka dauka a garin Maiduguri lokacin jana’izar wani Shehin Malami. CDD tana kira ga jama’a da watsi da bidiyon da kuma daina yadashi.

#AdainaYadaLabaranKarya #MuHadaHannuDakileYaduwarCutarCorona

Leave a Reply