Daraktan Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO Bai Bayyana Kamuwa Da Cutar Corona Ba!

Tushen Magana:

A ranar Litinin, 2 ga watan Nuwanban shekara ta 2020, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya Da Cigaba (CDD) sun gano yadda zaurukan yanar gizo da dama suka wallafa labarin cewa, babban daraktan hukumar lafiya ta duniya (WHO) ya kamu da cutar Corona.

Labarin wanda, shafukan yanar gizon suka wallafa cikin yanayin cewa labari ne da dumi-dumin sa sunyi ikirarin cewa daraktan ne da kansa wato Dr. Tedros ya bayyana hakanne a shafin sa na Twitter (@DrTedros).

Gaskiyar Magana:

Dr. Tedros baice ya kamu da cutar Corona ba a jawabin da ya wallafa a shafin na Twitter. Abinda Tedros din ya fada ranar Ladi, 1 ga watan Nuwanban da muke ciki shine cewa ya killace kansa bayan da yayi mu’amala da wani dake dauke da cutar ta Corona.

Zaurukan yanar gizo da yawa sun canza ma’ana ga abinda daraktan hukumar lafiya ta duniyar ya wallafa a shafin na Twitter kuma wannan jawabi da aka jirkita yana cigaba da yaduwa.

Karin abinda daraktan ya fada shine cewa bashi da alamu cutar bayan yayi mu’amala da mai dauke da ita, ga abinda ya wallafa acikin hoton a kasa (yayi bayanin ne a harshen turanci)

Ana killace kai ne idan ansamu cudanya ko mu’amala da mai dauke da cutar dan duba yiwuwar samun rashin lafiya.

Kammalawa:

Labarin da ake yadawa cewa daraktan hukumar lafiya ta duniya (WHO) ya kamu da cutar Corona karya ne!

Gaskiyar magana itace daraktan ya wallafa wani bayani a shafin sa na Twitter cewa ya killace kansa bayan yayi mu’amala da wadda ke dauke da cutar ta COVID-19 amma bawai ya kamu da cutar ba.

CDD tana jan hankalin jama’a game da yada labaran da basu da tabbacin sahihancin su. Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke shakku akansu dan tantance muku ta hanyar WhatsApp ko gajeren sako ta wannan lamba +2349062910568 ko a shafin Twitter a: @CDDWestAfrica ko @CDDWestAfrica_H

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa