Dan Takarar Jam’iyyar ZLP Ajayi Agboola Har Yanzu Yana Takarar Zama Gwamnan Jahar Ondo

Tushen Magana:

A ranar Asabat 10, ga watan Oktoban shekara ta 2020 masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano hoton wata takardar sanarwa da akayi zargin ta fito daga dan takarar jam’iyyar Zenith Labour Party (ZLP) a zaben gwamnan jahar Ondo da ake gudanarwa yau, wato Hon. Agboola Ajayi ya janye takararsa.

Gaskiyar Magana:

Labarin da ake yadawa cewa dan takarar gwamna na jam’iyyar Zenith Labour Party (ZLP) ya janye takarar da yakeyi na zama gwamnan jahar Ondo karya ne! hoton takardar da ake yadawa a shafukan sada zumunta na zamani bata fito daga dan takarar ko jam’iyyarsa ba.

Wata sanarwa dad an takarar ya wallafa a shafin san a Twitter mai dauke dasa hannun sakataren yada labarai na jam’iyyar ZLP din, Babatope Okeowo yace wasikar da aka yada cewa dan takarar ya janye batayi dai-dai da takardar da jam’iyyar take anfani da ita kuma bata dauke da saka hannun mai taimaka masa ta fuskar yada labarai.

Okeowo yace takardar da ake yadawa din ta bog ice dan haka mutane suyi watsi da ita.

Kammalawa:

Labarin da ake yadawa cewa dan takarar jam’iyyar Zenith Labour Party Hon. Agboola Ajayi ya janye takararsa karya ne.

CDD tana kira ga jama’a suyi watsi da labarin tare da daina yadashi.

#AgujiYadaLabaranKarya

Kuna iya aikowa CDD labarai ko bayanan da kuke da shakku akansu dan ta tantance muku sahihancin su. Zaku iya turo labaran ta wannan lamba: +2349062910568 ko a shafukan mu na Twitter a @CDDWestAfrica ko @CDDWestAfrica_H

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa