Cutar COVID-19: Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo Bai Bada Kyautar Naira Dubu Biyar (N5,000) Ga Kowane Dan Najeriya Ba.

Tushen Magana: Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba wato (CDD) ta gano wani bayani da aka wallafa a wani shafin yanar gizo dake ikirarin cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo zai bada naira dubu biyar (5,000) ga kowane dan Najeriya ta hanyar asusun ajiyarsa ko ajiyarta na banki tare da yin anfani da lambar kariyar su ta banki wato BVN.

Bayanin wanda ke cigaba da jan hankali musamman a yanar gizo wanda wani dandalin yanar gizo mai suna legitfund.ng ya wallafa an karanta shi sau dubu hamsin (50,000). Wannan bayanin har wayau ya lissafo wadansu masu rike da mukaman gwamnati da acewar sa sun aikata ayyukan rashawa, haka kuma inji shi wannan bayani tsohon shugaban kasa Obasanjo yana da kwarewa wajen tafiyar da kassar da cin hanci da rashawa ke wanzuwa.

Gaskiyar Magana: bayan gudanar da bincike, kwararru akan tantance bayanai da labarai na CDD sun fahimci cewa lambar kariya ko tsaro ta banki wato BVN lamba ce da bankuna kawai ke adana su ba tare da rabasu ga wassu mutane ba, kuma bankunan suna matukar kiyaye wannan lamba. Bankuna basa raba wannan lamba ta BVN ta mutane ga wassu mutanen, saboda haka yana da wahala ko ga tsohon shugaban kasa ya tattara BNV din duk yan Najeriya.

Binciken CDD har wayau ya gano cewa wannan labari na bogi ya samo asali ne daga wani jawabi da aka wallafa a shafin yanar gizo kuma ba’a zayyana tushen labarin ba.

Shafin yanar gizon da ya wallafa wannan labari na bogi mai alama legitfund.ng kwaikwayo ne da akayi na shafin legit.ng kuma masu gudanar dashi wancan shafi suna so ne kawai su ruda mutane ta hanyar nuna kamar cewa shafin nasu shine na legit.ng alhalin ba nashi bane.

Masu tantance sahihancin labari na CDD har wayau sun gano cewa labarin yayi kama da ire-irensa na bogi dake ikirarin cewa yan siyasa zamu raba kudi ga mutane inda kuma ake umartan mutanen su bada bayanan su da lambobin asusun ajiyar su na banki da lambar BVN dan abasu kudi.

Kammalawa:

Sahihin tallafin kudin da za’a rabawa mutane shine wanda za’a baiwa mutane masu rauni daga asusun jin kai da sunayen su ke cikin kundin tara bayanan mutane masu rauni na kasa. Wannan tallafi kuma ofishin mai’aikatar jinkai da bada dauki ne gudanar dashi. CDD tana jan hankalin jama’a da suyi watsi da duk wani labari ko bayani da bai fito daga majiyoyi masu tushe ba.

#AdainaYadaLabaranKarya

Leave a Comment

Your email address will not be published.