Cutar COVID-19: NCDC Bata Kashe Naira Biliya Daya Ba Dan Wayar Da Kan Yan Najeriya Ta Hanya Gajeran Sakon Waya (SMS)

Jita-Jitar Da Ake Yadawa: a ranar 8 ga watan Afirilun shekara ta 2020, Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba wato (CDD) ta gano wani labari da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani wanda yake bayyana cewa hukumar dakile yaduwar cutuka ta kasa Nigerian Centre for Disease Control (NCDC) ta kashe kudi har naira miliyan dubu daya dan wayar da kan yan Najeriya akan Cutar Corona, kamar yadda wannan labari na bogi ya zayyana, hukumar ta kashe kudin ne ta hanyar aikawa yan Najeriya gajeren sako ta waya wato SMS.

Jigon labarin wanda aka gina shi kamar haka: “Labari da dumi-dumin sa: Mun Kashe Naira Miliyan Dubu Ta Hanyar Turawa Yan Najeriya Gajeren Sakon Waya Dan Wayar Da Kansu Game Da Cutar Corona-Inji NCDC”, an yada wannan jigon labari a shafuka sada zumunta na Twitter da Facebook, da wassu shafukan yanar gizo.

Gaskiyar Magana: binciken kwakwaf da CDD ta gudanar ya gano cewa labari ne na bogi da wani shafi da ya saba wallafa labaru marasa tushe mai suna Reporters Press NG ya wallafa. Binciken CDD ya gano cewa an kirkiri shafin ne a ranar 8 ga watan Fabrairun shekara ta 2020 kuma daga kirkiran shafin zuwa yanzu, ya wallafa labaran bogi da yawa.

Kari akan batun, hukumar dakile yaduwar cutuka ta kasa NCDC tayi watsi da labarin inda ta bayyana shi a matsayin na bogi. A bayanin da ta wallafa a shafin ta na Twitter, NCDC tace: “kodayake wayar da kan yan kasa ta hanyar aika musu gajeren sako game da Cutar COVID-19 daya ne daga cikin hanyoyi masu muhimmaci da NCDC ke anfani dasu, yana da kyau asani cewa taimako ne da hukumar dakile yaduwar cutaka ta kasar ke samu daga kanfanonin sadarwa na Airtel Nigeria da MTN Nigeria da Globacom Nigeria dan yada wanna sako ga yan Najeriya”.

Kammalawa: Hukumar dakile yaduwar cutuka ta kasa NCDC bata kasha naira biliyan daya ba ta hanyar aikawa yan Najeriya gajeren sakon waya dan fadakar dasu game Cutar Corona. Labarin da ake yadawa musamman a yanar gizo labari ne na bogi. CDD tana jan hankalin yan Najeriya da su rika tantance labari musamman wanda ya shafi Cutar Corona kafin yadashi. #AdainaYadaLabaranBogi

Leave a Comment

Your email address will not be published.