Skip to main content

Tushen Magana:

Masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba wato CDD sunci karo da wata sanarwa da aka yada ta manhajar WhatsApp dake cewa hukumar gyaran hali ta kasa reshen Jahar Kano ta shirya dan sallamar fursononi dake tsare a hannunta, sanarwar ta kara da cewahukumar zata sake fursononin da suka kwashe kimanin shekaru uku ko fiye da haka a gidan gyaran halin reshen Jahar Kanon.

Sanarwar wadda aka tsarata cikin harshen Hausa ta bukaci mutane musamman wadanda ked a yan uwa a gidan gyaran halin da gabatar da lambar kotu da lambar zargin da ake yiwa yan uwan nasu da sake su ba tare da bata lokaci ba.

Ga abinda sanarwar ta kara da fada kamar haka: “duk wanda yake da dan’uwa ko yar’uwa dake garkame a daya daga cikin gidan gyaran hali na Jahar Kano kuma wannan dan’uwa nasa ya ko ta kwashe shekaru uku ko ka sama da haka ba tare da fuskantar shari’a ba, aturo lambar shari’ar sad a lambar kotun dake sauraron karar sad a fitar dashi kamar yadda Shugaban Kasa ya bada umarni. Atura bayanai ga wannan lamba 08067139558”

Gaskiyar Magana:

Masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba wato CDD sun tuntubi jami’in yada labarai da hulda da jama’a na hukumar gyaran halin ta kasa reshen jahar Kano, DSC Musbahu Lawan Kofar Nasarawa dan jin ba’asin sa game da sanarwar inda take ya bayyana sanarwar a matsayin aikin yan danfara masu aniyar zanbatar mutane yana mai bayyana cewa kwata-kwata sanarawar bata fito daga wajen suba.

Kofar Nasarawa yace: “a matsayina na jami’in hulda da jama’a na wannan huukuma a Jahar Kano, ni naked a hakkin sanar da jama’a duk wani bayani da zai fito daga gidajen gyaran hali, kuma ni ban bada wata makamanciyar wannan ba”.

DSC Musbahu yace basu san waye mai lambar da akace a tura bayanai dan sake fursononin ba dan haka suna kira ga mutane suyi watsi da sanarwa saboda rashin sahihancin ta, hasali ma bata fito daga hukumar gyaran hali reshen Jahar Kano ba.

Kammalawa:

Sanarwar da ake yadawa ta manhajar WhatsApp cewa hukumar gidan gyaran hali ta kasa reshen Jahar Kano na kira ga yan uwan fursononin da suka kwashe shekaru uku da su turo lambar kotun dake sauraron karar su da lambar karar tasu dan sake su karye ne! CDD na kira ga jama’a da suyi watsi da sanarwar da kuma daina yada ta.

Leave a Reply