Cutar Corona: Shin Katafaren Wajen Killace Masu Dauke da Cutar Corona Na Kano Ya Fara Aiki?

Gaskiyar Maga: Bai Fara Aiki Ba.

Tushen Magana:

A ranar Ladi, 23 ga watan Mayun shekara ta 2020 wani bidiyo da wani mutumin da ba’a san kowaye shi ba ya dauka kuma mutane da yawan gaske suka yadashi a manhajar WhatsApp ya bayyana cewa katafaren wajen killace masu dauke da cutar Corona dake filin wasa na Sani Abacha babu kowa acikin sa.

Bayan da yaje dakin was an na Sani Abacha inda ananne ake gina katafaren wajen killace mutanen, wanda ya nadi bidiyon ya bayyana cewa an dakatar da aiki a wajen. Wannan yaci karo bayanin gwamnatin Kanon cewa wajen bai fara aiki ba.

Wanda ya dauki bidiyon ya bayyana cewa acikin irin wannan mawuyacin hali ne ake kwantar da mutane a jahar Kano a wannan lokaci da ake yakar cutar Corona.

Har wayau wanda ya dauki bidiyon ya kara da cewa duk alkaluman da gwamnatin tarayya ke bayarwa akan cutar Corona a jahar Kano karya ne. Mutumin yace babu cutar Corona a Kano dama Najeriya baki daya.

Gaskiyar Magana:

Binciken kwakwaf da CDD ta aiwatar ya gano cewa gwamnatin Kano ta bada filin wasa na Sani Abacha ga Gidauniyar Dangote dan gina wajen killace mutanen da aka tabbatar cewa suna dauke da cutar Corona mai kimanin gadaje 213.

Ba kamara yadda wanda ya dauki bidiyon yayi ikirari ba, da yake maida martani, mai taimakawa gwamnatin Kano a ta fannin yada labarai Salihu Yakasai yace ba’a gaddamar da wajen killace masu dauke da cutar Coronar ba.

Yakasai yace wajen killace mutanen wanda har yanzu ba’a gama gininsa ba, dauki ne ko gudummawa da kungiyoyin sakai suke ginawa kuma har yanzu ba’a kamala aikinsa ba.

Salihu Tanko ya kara da cewa aikin ya tsaya ne sakamakon wani kuskure da aka gano ka iya kawo matsalakamar yadda suka fuskanci makamanciyar irin wannan matsala a jahar Lagos, kuma aiwatar da wannan gyara zai kare mjutane daga fuskantar ko kamuwa da cutar Corona.

Wani bayani da aka rabawa manema labarai da gangamin yakar cutra Corona din suka fitar ta bayyana cewa har yanzu cigaba da aiki a wajen killace mutanen.

Jawabin wanda Zouera Yousoufou, shugabar Gidauniyar Dangote ta sakawa hannu kuma CDD ta samu kofi ta bayyana cewa an nadi bidiyon ne dan kirkiran fitina.

Zouera tace gangamin yakara cutar Coronar ta yanke shawarar samar da wajen killace mutane masu dauke da cutar mai bangare guda biyu da kuma yake da adadin gadaje guda 500.

Ta kara da cewa gangamin ya samar da kayayyaki kamar su naurar taimakawa wajen numfashi, kayayyakin kariya ga ma’aikatan lafiya da dai sauran wassu mihmman kayayyaki kuma duk sunanan daki ajiye kayayyaki na ma;aikatar lafiya ta jahar Kano har zuwa lokacin da za’a kamala aikin.

Zouera Yousoufou ta kara da cewa an samu jinkirin kamala aikin ne sakamakon dokar zama a gida dake cigaba da wanzuwa saboda fitowar masu aikin yana da dan wahala amma duk lokacin da aka kamala aikin kuma za’a kaddamar dashi za’a sanar da hakan.

Har wayau, ba kamar yadda wanda ya dauki bidiyon yayi ikirari ba, binciken CDD ya gano cewa kawo ranar 15 ga watan Mayun shekara ta 2020, ansamu bullar cutar Corona a jahar Kano har sau 919 a jahar Kano kamar yadda kiyasin hukumar dakile yaduwar cutuka ta kasa NCDC ta wallafa a shafin tan a yanar gizo. Binciken CDD ya gano cewa jahar Kano itace ta biyu a yawan masu dauke cutar Corona bayan jahar Lagos wadda take da masu dauke da cutar har 3595

Kammalawa:

Jita-jitar da ake yadawa cewa wajen killace masu dauke da cutar Corona dake filin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata acikin garin Kano yana aiki amma babu masu dauke da cutar karya ne. har wayau ikirarin wani bidiyo yayi cewa babu masu Corona a jahar Kano shima karya ne.

Kuna iya turo wa CDD sakonni da labaran da kuke da shakku akansu dan tantance sahihancin su ta wannan lamba: +2349062910568 ko ku tuntunbe mu a shafin mu na Twitter mai adireshi kamar haka: @CDDWestAfrica_H.

Leave a Comment

Your email address will not be published.