Skip to main content

Tushen Magana:

A ranar 22 ga watan Afirilun shekara ta 2020 masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya Da Cigaba (CDD) sukaci karo da wata sanarawa da ake rabawa yan jarida wadda tayi ikirarin cewa ma’aiakatar ilimi ta kasa tace an rufe makaratu a fadin kasa baki daya kuma baza a bude su dan cigaba da karatu ba har sai watan Nuwanban wannan shekarar ta 2020 da ashirin da muke ciki sakamakon annobar cutar Corona da ake fama da ita yanzu haka.

Sanarwar wadda dubban mutane suka ganta mai dauke da kwanan wata 21 ga watan Afirilun shekara ta 2020 an danganta ta ministan ilimi Malam Adamu Adamu da kuma wata sa hannu mai kamar nasa.

Gaskiyar Magana:

A ranar 19 ga watan Maris din shekara ta 2020 ma’aikatar lafiya ta kasa ta bada umarnin rufe dukkan makarantu a fadin Najeriya baki daya sakamakon tabbatar bullar cutar Corona.

Binciken da CDD ta gudanar a shafin yanar gizon ma’aikatar lafiya ta tarayya ya gano cewa ma’aikatar bata fitar da kowace sanarwa dake bada umarnin cewa sai watan Nuwanba a bude makarantu ba.

Sanarwar da aka yada din ta bayyana cewa babban sakatare a ma’aikatar ilimi ta kasa Mr. Sunny Echono shine ya tabbatar wa jairdar Premium Times da ake wallafawa a yanar gizo bude makarantun da za’ayi a watan Nuwanba, amma editan jaridar Idris Akinbajo ya gayawa masu tantance sahihancin labarai na CDD cewa batun bude makarantu a watan Nuwanban magana ce maras tushe kuma aiki ne na wassu bata gari.

Mr. Akinbajo ya kara da cewa wanda suka kirkiri labari bogin sun dauki wani labari makamancin wannan da jaridar Premium Times din ta wallafa a shekarar data gabata sannan suka sauya masa fasali dan cimma bukatar su.

Wata alama ta nuna cewa sanarwar ta bogi itace yadda sanarwa da ake rabawa ga manema labaran ta jinjigina kanta da wata jarida abinda baya faruwa.

Acikin sanarwar an bayyana cewa Adamu Mallam ne ya saka hannu akanta, kuma sunan ministan ilimin Najeriya shine Malam Adamu Adamu.

Lokacin da yake yiwa manema labarai jawabi game da batun ranar 21 ga watan Afirilun shekara ta 2020, karamin ministan ilimi Emrka Nwajiuba yace har yanzu ma’aikatar ilimin bata cimma matsaya ba game da ranar bude makarantun.

Ministan ya cigaba da cewa “daga mun cimma matsaya akan ranar da za’a bude makarantun zamu sanar, kunsan mun rufe makarantun ne a karshen watan Maris saboda barkewar cutar Corona”.

Ministan ya kara da cewa bude makarantun al’amari ne na hadaka da zai shafi dukkan jihohi saboda akwai jihohin da dokar hana fita.

Kammalawa:

Sanarwar da ake yadawa cewa ma’aikatar ilimi ta tarayya zata bude makarantu a atan Nuwanban shekara ta 2020 labari ne na bogi. Ma’aikatar ilimin bata fitar da kowace sanarwa akan bude makarantu ba kawo yanzu. CDD tana kira ga iyaye da dalibai da dukkan jama’a da suyi watsi da wannan sanarwar.

Leave a Reply