Babu Wani Tsarin Bada Tallafi Daga Gidauniyar Dangote

Tushen Magana:

A ranar Talata, 16 ga watan Fabrairun shekara ta 2021, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani sakon da ake yadawa ta manhajar WhatsApp da ke ikirarin cewa Gidauniya Aliko Dangote na bada tallafi dan fara sana’o’i gay an Najeriya da suka cancanta.

Sakon yace: “Ku gaggauta dubawa dan sanin ko kun cancanta da samun tallafin kudi daga tsarin bada tallafi na Gidauniyar Dangote na shekara ta 2021”

Gaskiyar Al’amari:

Binciken da CDD ta gudanar game da ikirarin tallafi daga Gidauniyar Dangoten ya gani cewa sakon da ake yadawa din sakon karya ne.

Adireshin yanar gizon da aka bayar dan yi rijista adireshi ne na bogi.

Hoton da aka lika a jikin sakon babu shi a adireshin yanar gizon da aka bayar dan yin rijistar, hakan kuma wani sabon salo ne na jan hankali da yaudaran mutane tare da zambatar su.

Karin binciken da CDD ta gudanar game da hotunan da biye da sakon ya gano cewa hotuna ne da aka dauka lokacin da Ministar Jinkai da Bada Dauki ga Jama’a, Sadaiyya Farouk take bada tallafin kudi ga yan Najeriya a watannin baya.

Hotunan an dauke su ne a yankin Kwale da ke kewayen babban birinin tarayya Abuja yayin raba kudi dan rage radadin zaman gida da fatattakar cutar Korona a watan Afirilun 2020.

Yayin rijistar ana bukatar masu neman tallafin su bada bayanan asusun su na banki, da lambar BVN, wannan kuma wata hanya ce day an damfara ke amfani da ita dan zambatan jama’a.

Wani sabon salo da wannan sakon bogi ke dauke dashi shine dokoki da ka’idoji day an damfarar suka tsara.

Nazarin da CDD ta aiwatar a shafin Gidauniyar Aliko Dangote dama shafin yanar gizon kamfanin nasa sun gano cewa sakon yanar gizon da aka yada game da su ba gaskiya bane.

Kawo lokacin hada wannan rahoto tallafin da Gidauniyar Dangote ke bayar shine ga mata da matasa kuma bayanan da muka samu sun nuna cewa Gidauniyar ta kammal raba kusan miliyan dubu hudu a jahohi sha daya, kuma wannan rabo zai cigaba a sauran jahohin Najeriya.

Kammalawa:

Wani sako da ake yadawa ta manhajar WhatsApp da ke cewa Gidauniyar Aliko Dangote na bada tallafin kudi ga yan Najeriya masu sa’a dan fara sana’o’i a shekara ta 2021 sako ne na bogi. Yan damfara kan tsara ire-iren wadan nan sakonni da nufin tattara bayanan mutane dan zambatan su a karshe.

CDD na jan hankalin jama’a da su tantance labarai ko sakonnin yanar gizo kafin amincewa ko aiwatar wani umarni. Mutane a kodayaushe su rika taka-tsantsan game da biya kudade ta hanyar yanar gizo musamman dan neman tallafi.

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa