Babu Wani Tsarin Bada Data Da N10,000 Kyauta Ga Masu Amfani Da Wayar Salula!

Gaskiyar Al’amari: Damfara Ce

Tushen Magana:

A ranar 31 ga watan Janairun shekara ta 2021, masu bin diddigin labarai da sakonni da gano gaskiyar su na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani sakon da ake yadawa ta manhajar WhatsApp. Sakon na cewa hukumar yin katin dan kasa tana bada tsarin shiga yanar gizo kyauta ga dukkan wadan da suka tantance lambobin wayoyin su.

Sakon mai lakabin “NINVerification” yayi ikirarin cewa hukumar yin katin dan kasa zata bada kyautar data da yawan ta yakai “5G” ga dukkan masu amfani da layin waya da suka wuce tsawon watanni uku suna amfani dashi.

Wani bangare na sakon yace: “ku duba idan kuna daga cikin wadan da zasu ci garabasar kyautar “5G” na data. Wannan tsari ne na kyautatawa ga dukkan wadan da sukayi amfani da layin wayar su har na tsawon watanni uku. Ga tsawon lokacin da za’a dauka ana bada garabasar: 30-01-2021 2021-2-29 “

Acikin wannan sako akwai wani adireshi na yanar gizo da aka bayar ga masu neman garabasar dan ziyarta su nuna sha’awar su.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa ikirarin bada garabasar data har ta “5G” din karya ne. kawai wasu mazambata ne ke tsara ire-iren wadannan sakonni dan cutar jama’a, amma babu wani tsari daga hukumar yin katin dan kasa na bada data kyauta ga masu amfani da layin wayar salula.

Binciken CDD har wayau ya bankado irin yadda aka tsara rufta jama’a ta hanyar bukatar su da su bayanan su a matakai uku tare da neman su kara yada wannan sako a zaurukan WhatsApp dan sauran mutane su gani.

Idan mutum ya fara bada bayanan sa za’a kara yi masa alkawarin naira dubu goma (N10,000) tare da bashi data mai yawan “5G”.

Wadannan mayaudara sun wallafa wasu bayanai na bogi da ke nuna yadda wasu mutane suka gwada tsarin kuma suka samu gamsuwa.

CDD ta kara gano wani gargadi da hukumar yin katin yan kasa ta wallafa a shafin tan a yanar gizo inda tace mutane suyi hankali wajen yarda da labaran bogi game da ta.

Kammalawa:

Sakon da ake yadawa cewa hukumar da ke yin katin dan kasa NIMC na bada data har “5G” da N10,000 ga masu amfani da wayar salula karya ne. Wadan su bata-gari ne suka kirkiri sakon kuma suke yadashi dan damfaran jama’a, dan haka a kula.

CDD na jan hanakalin jama’a da cewa su guji kirikira ko yada labarai ko sakonni na karya.

Kuna iya aikowa CDD labarai ko sakonnin da kuke da shakku akansu dan tantance muku sahihancin su ta wannan lamba +2349062910568, kuna ma iya aiko sakon WhatsApp.

#AgujiYadaLabaranKarya

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa