Babu Wani Shirin Tallafin N30,000 Da Shirin N-Power ke Baiwa Yan Najeriya a Wannan Lokaci

Tushen Magana:

A ranar Talata, 29 ga watana Dismaban shekara ta 2020, masu bin diddigin labarai da bayanan da ake yadawa na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani sako da aka wallafa kuma ake yadawa a shafuka sada zumunta zamani, sako na ikirarin cewa ana bada tallafin naira 30,000 ga yan Najeriya, acewar sakon, shirin N-Power ne ke bada wannan tallafi ga yan Najeriya. An wallafa wani adireshin yanar gizo tare da sakon inda aka bukaci mutane su ziyarta tare da bada bayanan su.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa babu wani shiri da N-Power ke aiwatarwa na bada tallafin naira 30,000 ga yan Najeriya. Yan danfara ne kawai suka tsara sakon da cutar jama’a.

CDD har wayau ta gano cewa adireshin yanar gizon da aka bayar din yana kama da na shirin N-Power gwamnatin tarayya amma ba nasu bane.

Binciken CDD din har wayau ya gano cewa sakon yayi anfani da yan danfarar yanar gizo ke anfani dashi na bukatar masu neman tallafin su bada bayanan asusun ajiyar su na banki da kuma gaya wa wassu mutanen 12 game da shirin tallafin kafin kammala cika fom din yanar gizon.

Kammalawa:

Wani sako da aka wallafa kuma ake yadawa a shafukan yanar gizo cewa shirin N-Power na raba tallafin naira dubu talatin (N30,000) ga yan Najeriya sako ne na bogi, dan haka CDD na jan hankalin jama’a da su kula kada su fada hannun yan danfara.

CDD tana jan hankalin mutane game da yada labarin bogi. Ku tabbatar da sahihancin labarai ko bayanan da kuke samu kafin ku yada su.

Zaku iya aikowa CDD sakonnin da kuke da shakku a kansu dan tantance muku su ta wannan lamba +2349062910568 ko shafin Twitter: @CDDWestAfrica @CDDWestAfrica_H

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa