Babu Wani Magani da Hukumar Kula Da Ingaancin Abinci da Magunguna ta Kasa NAFDAC ta Amince Dashi a Matasyin Maganin Cutar Corona

Tushen Magana:

A ranar 11 ga watan Yulin shekara ta 2020, wassu zauruka da yawa na yanar gizo a Najeriya sun rawaito cewa hukumar kula da ingancin magunguna da abinci ta kasa NAFDAC ta amince da PAX a matsayin maganin da zai bada garkuwa ga mutane daga kamuwa da cutar Corona.

Rahotannin da aka wallafa sun bayyana cewa Daraktan wani wajen samr da maganin garjiya ake kira Pax Herbal Clinic and Research Laboratories, Reverend Father Anslem Adodo ne bayyana samun amincewa da maganin a matsayin kariya daga cutar Corona.

Wannan ikirarin samun maganin cuta ta Corona jaridar The Guardian Nigeria ta wallafa shi yayin da wassu kafafen sada zumunta na zamani suma suka yadashi.

Gaskiyar Magana:

Hukumar kula da inganci magunguna da abinci ta kasa NAFDAC bata amince da PAX herbal a matsayin maganin cutar Corona ba.

Paxherbals, wanda akafi sani da Pax Herbal Clinic and Research Laboratories, an kafa shi ne a 1996 kuma wanda ya kafashi shine Adodo Anselm. Kanfanin kanfani ne dake samar da magungunan gargajiya.

A martanin day a mayar game da batun, daraktan hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC, Farfesa Moji Adeyeye tace ikirarin da akayi cewa NAFDAC din ta amince da Pax Herbal a matsayin maganin da zai bada kariya daga cutar Corona bai tabbata ba.

Farfesa Adeyeye tace Pax Herbal sun nemi NAFDAC ta amince da kafso mai nauyin 290mg mai suna Pax Herbal Cugzin tare da tabbatar da cewa za’a iya anfani dashi ba tare da wata matsala ba.

Ta kara da cewa, kanfanin da ya samar da maganin yayi ikirarin cewa yana kar karfin garkuwar jiki.

Fake News Alert! 5 Steps to Verify Every Information on CDD Channel

Farfesa Adeyeye ta cigaba da cewa kodayak hukumar tace ana iya anfani da maganin amma gargadi da yake jikin kwalin sa ya zayyana karara cewa har yanzu NAFDAC bata gama binciken tan a kwa-kwaf ba akan maganin.

Adeyeye har wayau ta kara da cewa jita-jitar da ake yadawa a dandalin sada zumunta ko kafafen sadarwa na zamani cewa NAFDAC ta amince da Paxherbal dan ya magance alamomin cutar Corona hakan bai tabbata ba

Kammalawa:

Labarin da ake yadawa cewa NAFDAC ta amince da wani magani da kafanin hada magunguna mai suna Pax Herbal Clinic and Research Laboratories ya samar na bada garkuwa daga kamuwa da cutar Corona karya ne.

Yana da kyau mu sani cewa kawo yanzu babu wani magani na gargajiya ko wanda binciken masana ya samar dashi da zai bada kariya daga cutar Corona. Abinda yafi muhimmanci mu sani shine bada tazara tare da tsaftace muhalli da jikin mu akai-akai sune abubuwan da zasu iya bamu kariya daga kamuwa da cutar Corona.

CDD tana jan hankalin mutane da akodayaushe su rika tantance labari kafin yadashi.

Kuna iya turowa CDD labaran da kuke da tantama akansu dan tantancewa ta wannan lambar: +2349062910568 ko shafin mu na twitter: @CCDWestAfrica, @CDDWestAfrica_H

#AdainaYadaLabaranKarya

Leave a Comment

Your email address will not be published.