Babu Mai Dauke Da Cutar Corona a Asibitin FMC Azare

Jita-jitar da ake yadawa:

Akwai wani labari na bogi da ake yadawa musamman ta manhajar WhatsApp dake gargadin mutane game da wani mai dauke da Cutar Corona da yake asibitin gwamnatin tarayya (Federal Medical Centre) dake garin Azare a jahar Bauchi. Labarin bogin ya ja hankalin mutane da suyi taka tsan-tsan game da asibitin saboda mai dauke da kwayar cutar ya dawo ne daga garin Legas kwana uku da suka wuce.

Gaskiyar Magana:

Masu tantance labari na CIbiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba wato CDD sunbi diddigin wannan jita-jita inda suka gano cewa labari ne kirikirarre kuma marar tushe. Majiyoyin da CDD ta tattauna dasu sun bayyana cewa labari na bogi da aka kirkireshi dan saka shakku a zukatan mutane game da asibitin. Har wayau CDD ta gano cewa mutum takwas (8) ne aka samu billar Cutar COVID-19 din a jikin su a fadin jahar Bauchi baki daya kuma dukkaninsu suna asibitin kowarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa dake garin Bauchi inda aka killace su kuma ake cigaba da basu kulawa.

Kammalawa:

 Labarin da ake yadawa cewa ansamu billar Cutar Corona a asibitin FMC dake garin Azare a jahar Bauchi labari ne na bogi. CDD tana kira ga jama’a da suyi watsi da wannan kirkirarren labari tare da daina yadashi. Kawo ranar sha hudu 14 ga watan Afirilun shekara ta 2020, masu dauke da kwayar cutar su takwas (8) ne a jahar Bauchi kuma dukkaninsu suna killace dan samun kulawa a garin Bauchi, saboda haka CDD na kira da a guji kirkira ko yada labaran karya.

Leave a Comment

Your email address will not be published.