Babu Daya Daga Cikin Likitocin Kasar China Da Suka Zo Dake Dauke Da Cutar Corona

Tushen Magana: wani labari da aka dauki hoton sa da kuma aka wallafa a shafin Twitter a wani dandali mai suna (@FRNcitizen) wadda kuma ake cigaba da yadawa ta manhajar WhasApp da sauran shafukan sada zumunta ya bayyana cewa: daya daga cikin likitoci guda goma sha biyar (15) da kanfanin gine-gine mai suna China Civil Engineering Construction Company (CCECC) ya turo Najeriya dan tallafawa wajen dakile Cutar Corona yana dauke da ita Cutar Corona din.

An gina labarin kamar haka, “Labari da dumi-dumin sa: ansamu daya daga cikin likitocin China da suka zo Najeriya da dauke da Cutar Corona. Wayyo”

Gaskiyar Magana: a ranar tara ga watan Afirilun shekara ta 2020, ayarin kwararrun masana a fannin lafiya da suka hada da likitoci, masu kula da marasa lafiya dama masana akan gwaji a dakin bincike na kasar Chaina suka iso Najeriya dan taimakawa kasar a yunkurin ta na dakile yaduwa da kawar da Cutar Corona.

Binciken da masu bin diddigin labari dan gano sahihancinsa na CDD suka aiwatar ya gano cewa labarin wadda wani dandali mai suna FRNCitizen a Twitter ya wallafa wanda kuma kawo karfe 11:58 na safiyar ranar 14 ga watan Afirilun shekara ta 2020 wassu mutane suka yadashi har sau dubu daya da saba’in da uku (1073) yayinda wassu mutanen da yawan su yakai dubu daya da dari hudu da ashirin da biyu (1422) suka bayyana farin cikin su game da wannan labari kodayake yanzu an cire wannan labari daga dandalin Twitter baki daya.

Har wayau binciken CDD ya gano cewa an wallafa labarin a shafin sada zumunta na Facebook kuma an yadashi sau saba’in da biyar (75) yayinda aka bada ba’asi har sau arba’in da takwas (48) akansa, anyi mu’amala sau 94 kawo tsakiyar ranar 16 ga watan Afirilun shekara 2020.

Wani bayani mai muhimmanci da binciken CDD ya gano game da wannan labari na bogi shine, wanda suka rubata labari sun gaza bayyana tushe ko inda suka samo labarin, kuma har yanzu babu wata kafar yada labarai yardajjiya da ta wallafa wannan labari na cewa daya daga cikin likitocin Chinan yana dauke da Cutar COVID-19.

Kari akan haka shine bayanin da hukumar dakile yaduwar cutuka ta kasa Nigerian Centre for Disease Control (NCDC) ta fitar inda tayi watsi da labarin inda ta bayyana shi a matasyin labarin bogi. A jawabin da NCDC din ta fitar a ranar Laraba 16 ga watan Afirilun shekara ta 2020 tace “jita-jitar da ake yadawa cewa daya daga cikin likitocin da aka kawo dan taimakawa Najeriya yakar Cutar COVID-19 yana da dauke da kwayar cutar karya ne”

NCDC a cikin bayanin ta kara da cewa Cutar Corona bata da alaka da yare ko kabilar mutum saboda haka mutane suyi watsi da rudu da jita-jita.

A wani martani makamancin wannan, kwamitin shugaban kasa akan Cutar CVOID-19 din shima yayi watsi da labarin inda ya bayyana shi a matsayin na bogi. Da yake magana a yayin jawabin kullum-kullum da kwamitin shugaban kasa akan Cutar COVID-19 din da ya gabata ranar Laraba 16 ga watan Afirilun shekara ta 2020, Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Muhammed ya bayyana labarin da cewa kirkirarren labari ne kuma marar tushe.

Kammalawa: Jita-jitar da take yawo cewa daya daga cikin likitocin kasar China da suka zo Najeriya dan taimakawa wajen yakar Cutar Corona yana dauke da cutar karya ne dan babu wata hujja data tabbatar da hakan. CDD tana jan hankalin mutane da su guji yada labaran karya. Yada labaran karya na haifar da illoli da yawa, dan haka CDD ke jan hankali game da kirkira ko yada labaran bogi.

#AdainaYadaLabaranKarya


Leave a Comment

Your email address will not be published.