Babbar Kotun Abuja Bata Dakatar Da Takarar Seriake Dickson Ba Sakamakon Zargin Gabatar Da Takardar Bogi

Tushen Magana:

CDD ta gano wani sako da aka yada ta manhajar WhatsApp da dandalin Facebook a ranar 13 ga watan Nuwanban shekara ta 2020 dake cewa babbar kotun tarayya dake zaman ta a Abuja ta dakatar da Hon. Seriake Dickson daga tsayawa takarar zamowa sanata mai wakiltar yamma cin jahar Bayelsa, kamar yadda wannan sako ya zaiyana dakatarwar ta biyo bayan samun sanatan ne da gabatar da takardar jebu.

Dickson shine gwamnan Bayelsa da ya sauka babu dadewa kuma yanzu haka yana takarar zamowa sanata a jam’iyyar PDP mai wakiltar Bayelsa ta yamma.

Ga sakon cikin hoto a kasa:

Gaskiyar Magana:

Bincken da CDD ta aiwatar ya gano cewa kotu bata dakatar da takarar Seriake Dickson ba. Hasalima mai sauraron karar Justice Jane Nyang yayi watsi ne da karar da aka shigar akan tsohon gwamnan saboda rashin hurumin kotun na sauraron karar.

Kotun ta kara da cewa an shigar da karar a kurarren lokaci saboda haka ba zata saurare ta ba.

Tun farko dan takarar jam’iyyar APC Eneoriekumoh Owoupele, ya gurfana a gaban kotun inda ya nemi ta dakatar da Dickson saboda abinda ya bayyana a matsayin gabatar da bayanai na jebu ga hukumar zabe ta kasa INEC da yace Dickson din yayi.

Sakon WhatsApp din da aka yada din yace babbar kotun Abuja ce ta ta dakatar da takarar Seriake Dickson, amma binciken da CDD ta aiwatar ya gano cewa babbar kotun Abuja ta mayar da karar jahar Bayelsa inda acan ne aka bada hukuncin da bayyana shigar da karar a kurarren lokaci.

Kammalawa:

Kotu bata dakatar da takarar tsohon gwamnan jahar Bayelsa, Hon. Seriake Dickson na zamowa sanata mai wakiltar yammacin jahar Bayelsa ba. Har yanzu Dickson yana takarar zama sanatan Bayelsa ta yamma.

CDD tana jan hankalin jama’a game da yada labaran da basu da tabbacin sahihancin su. Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke shakku akansu dan tantance muku ta hanyar WhatsApp ko gajeren sako ta wannan lamba +2349062910568 ko a shafin Twitter a: @CDDWestAfrica ko @CDDWestAfrica_H

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa