Ba’a Yankewa Kwamishina a Jahar Edo Hukuncin Daurin Shekaru Goma a Gidan Yari Ba!

Tushen Magana:

A ranar Laraba, 10 ga watan Satunban shekara ta 2020, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sukaci karo da wani sako da ake yadawa a manhajar WhatsApp cewa Osaze Osemwegie-Ero wanda kwamishinan al’adu da bude ido da kuma harkokin ketare a jahar Edo an yanke masa hukuncin daurin shekaru goma a gidan yari.

Sakon wanda ya farad a jigo kamar haka: “Labari da dumi-duminsa: hukuncin daurin shekaru 10 yahau kan Osaze Osemwegie-Ero, kwamishinan ma’aikatar al’adu da bude ido da harkokin ketare na jahar Edo”. Hukuncin ya biyo bayan rashin nasara da kwamishinan yayi bayan daukaka kara a ranar Laraba, 9 ga watan Satunban 2020.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa ba’a yankewa Osemwegie-Ero hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru goma ba kamar yadda ake yadawa a manhajar WhatsApp. Babu daya daga cikin manyan jaridun Najeriya da ta rawaito wannan labari.

A watan Nuwanban shekara ta 2019 yan sandan kasa-da-kasa na kasar Faransa sun kama Osemwingie-Ero bisa zargin almundahanar kudade da yawansu yakai dala miliyan biyu.

Hukumar yakar cin hanc da rashawa ta Najeriya wato Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) ta tabbatar kama Osemwingie-Ero.

Duk cewa ba’a gabatar da shaidun aiwatar da jita-jitar hukuncin tura kwamishinan gidan yari ba, jami’in yada labarai na jam’iyyar PDP a jahar Edo ya bayyana labarin hukunta kwamishinan a matsayin na bogi.

Da yake yiwa CDD Karin bayani, Nehikhare yace har yanzu ba’a saka ranar sauraron zarge-zargen da ake yiwa kwamishinan ba. Ya kara da cewa ahalin yanzu Osemwegie-Ero ba shine kwamishinan ma’aikatar al’adu da bude da harkokin ketare.

Kammalawa:

Sakon da ake yadawa cewa an yankewa Osaze Osemwegie-Ero na jahar Edo hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari karya ne! Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa wannan labari ne na bogi.

CDD tana jan hankalin mutane da su guji kirkira da yada labaran karya kuma akodayasuhe su rika tantance sahihancin labarai kafin yadasu

Zaku iya aikowa CDD labaran da kuke da shakku akansu domin tantance muku sahihancin su. Kuna iya aikowa ta wannan lamba +2349062910568 ko ta adireshin mu na Twitter a @CDDWestAfrica.

#AgujiYadaLabaranKarya

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa