Ba’a Nada Tsohon Gwamnan Bauchi Ahmed Adamu Muazu a Matsayin Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa na Riko Ba

Tushen Magana:

A ranar Juma’a, 13 ga watan Nuwanban shekara ta 2020, masu bin diddigin labarai dan gani sahihancin su na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani labari da wata jarida ta wallafa kuma ake yadashi a manhajar WhatsApp.

Labarin wadda jarida mai suna CityNews ta wallafa shi ya buga hoton tsohon gwamnan jahar Bauchi, Ahmed Adamu Muazu a matsayin sabon shugaban hukumar zabe ta kasa na riko.

Taken labarin shine: “Labari da dumi-dumin sa: Muazu ya zama shugaban INEC na riko”.

Gaskiyar Magana:

Ba’a nada tsohon gwamnan jahar Bauchi Ahmed Adamu Muazu a matsayin shugaban hukumar zabe ta kasa INEC na rikon kwarya ba.

Bincikne da CDD ta aiwatar ya gano cewa jaridar CityNews cikin kuskure ta wallafa hoton Ahmed Adamu Muazu a matsayin shugaban da zai jagoranci hukumar zaben na wucin-gadi bayan da wa’adin wanda ke kan kuejer Farfesa Mahmoud Yakubu ya kare.

Adaidai lokacin da wa’adin Farfesa Yakubu na karon farko yak are, ya mika ragamar INEC din zuwa ga daya daga cikin kwamishionin ta dan asalin jahar Gombe, wato Air Vice Marshal Ahmed Muazu.

CDD ta gano cewa wadda zai jagoranci hukumar zaben shine AVM Ahmed Muazu wadda daya ne daga cikin kwamishinonin hukumar zaben.

Mutumin da aka buga hoton sa a matsayin shugaban hukumar na riko wato toshon gwamnan jahar Bauchi Ahmed Adamu Muazu bashi da laka da hukumar zaben ta kasa INEC. Hasalima yayi gwamnan Bauchi ne daga shekarar 1999 zuwa 2003.

Kammalawa:

Labarin da ake yadawa cewa an nada tsohon gwaman jahar Bauchi Ahmed Adamu Muazu a matsayin shugaban hukumar zabe ta kasa INEC na rikon-kwarya karya ne.

CDD tana jan hankalin jama’a game da yada labaran da basu da tabbacin sahihancin su. Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke shakku akansu dan tantance muku ta hanyar WhatsApp ko gajeren sako ta wannan lamba +2349062910568 ko a shafin Twitter a: @CDDWestAfrica ko @CDDWestAfrica_H

#AgujiYadaLabaranBogi

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa