Ba’a Kaiwa Ayarin Motocin Gwamnan Borno Hari Ba

Tushen Magana:

A ranar Ladi, 22 ga watan Nuwanban shekara ta 2020, masu bin diddigin sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani labari da jaridar Sahara Reporters suka wallafa inda sukace yan ta’adda sun kaiwa ayarin motocin gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum hari.

Kamar yadda labarin ya zayyana, yan ta’addan sunyi kwantan baune ne ga ayarin farko na motocin dake rakiyar Gwamna Zulum din a ranar Asabat, 21 ga watan Nuwanban shekara ta 2020 a Ja’alta dake kan titin Gajiram zuwa Munguno.

Labarin har wayau yace an kasha sojoji bakwai da jami’an tsaron kato-da-gora a lokacin da suke kan hanyar su ta zuwa Baga dake karamar hukumar Kukawa.

Gaskiyar Magana:

Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa ba’a kawai ayarin motocin Gwamna Babagana Umara Zulum hari ba. Hasalima mai magana da yawun gwamnan, Isa Gusau yace babu wanda yakai musu hari.

A wata sanarwa da ya fitar, Gusau yace babu wanda ya fuskanci kowane irin hari tsakanin Gwamna Zulum ko ayarin motocin sa duk kuwa da cewa Sahara Reporters sun rawaito faruwar hakan, amma al’amarin bai faru ba.

Isa Gusau yace: “muna son mu tabbatar da cewa wani labari da wata kafar yada labarai ta yanar gizo ta wallafa cikin sigar ‘labari da dumi-dumin sa’ cewa an kaiwa Gwamna Zulum hari karya ne”

“kamar yadda jama’a suka sani Zulum mutum ne mai kallon abubuwa a yadda suke kuma fade su a yadda suke, a wannan karon babu hari da aka kai masa”

Kari akan bayanin Isa Gusau shie babu wata kafar yada labarai sahihiya da ta rawaito faruwar al’amarin, kuma wannan wata alama ce dake nuna rashin faruwar al’amarin.

Kammalawa:

Labarin da ake yadwa cewa an kaiwa ayarin motocin Gwamna Babagana Umara Zulum na jahar Borno hari karya ne. Har wayau labarin da jaridar Sahara Reporters ta wallafa cewa an kai hari ga jami’an tsaron dake baiwa Gwamnan kariya ne!

CDD tana jan hankalin jama’a game da yada labaran da basu da tabbacin sahihancin su. Kuna iya aikowa CDD labaran da kuke shakku akansu dan tantance muku ta hanyar WhatsApp ko gajeren sako ta wannan lamba +2349062910568 ko a shafin Twitter a: @CDDWestAfrica ko @CDDWestAfrica_H

Center for Democracy and Development West Africa| CDD West Africa