Shin Turiri Dake Fitowa Bayan An Dafa Lemon Tsami da Uda da Uziza Yana Maganin Cutar Coronavirus?

Gaskiyar Magana: Hakan Bai Tabbata Ba.

Ga abinda wani bangare na wata jita-jita da ake yadawa yake cewa: Kanwar surukar wata mata mai suna Nwunye mai’aikaciyar jinya ne a Birnin New York dake kasar Amurka kuma ta kamu da cutar COVID19. A lokacin da take jiran sakamakon gwajin da akayi mata na cutar sai mijinta da ya’yanta suka dauki cutar Coronavirus din daga wajenta. Saboda rashin gado a asibiti, sai akayi jinyar ta a gida. Mijinta ya dafa Uda, Uziza, Lemon Tsami da kuma Citta ya rufe su acikin tawul sai ya bata ta shaki turirin. Yanzu zance da akeyi duk sun warke daga cutar Coronavirus. Toh, sai ku sayi Uda da Uziza da Lemon Tsami da Citta ku ajiye a gida saboda suna maganin cutar Coronavirus”.

Wannan sako an yada shi sosai a tsakanin yan Najeriya musamman wanda suke yankin Kudu Maso Gabas (yan kabilar Igbo) ta manhajar WhatsApp.

Gaskiyar Magana:

A lokutan da ake fama da annobar da ta shafi lafiya a duniya kamar irin wanda a fuskanta yanzu, saboda fargaba da mutane suke ciki, mutane kanyi yunkurin samarwa kansu magani da kansu ta hanyar anfani da tunaninsu saboda tsirar da rayuwar su.

Kodayake yan Najeriya musamman yan kabilar Igbo suna ganin cewa wannan hanyace ta warkar da cututtuka, har yanzu sahihin bincike bai kai ga gano cewa wannan hanya tana maganin cutar Coronavirus ba.

A al’adar Igbo, bin wannan hanya ta anfanin da Uda da Uziza kamar yadda wannan jita-jita ta zayyana anyi ittifakin cewa yana maganin cututtuka da yawa da matsalolin rashin lafiya da suka lafiyar mai jego post-natal care.

Magungunan bature da yawa sun samo asali ne daga tsirrai, magungunan da suka shafi kunburin ciki, nunfashi, zazzabi, kwayoyin cuta da dai sauransu.

Masu bincike a bangaren lafiya sun bayyana cewa bawon itatuwa musamman na kayan marmari kamar su lemo, lemon tsami da dangoginsu suna taka rawa wajen warware wassu matsalolin da suka shafi lafiya, amma bincike bai-kai ga tabbatar da ingancinsu wajen maganin cututtuka masu yaduwa ba, hakanan binciken bai gano cewa zasu iya maganin cutar COVID-19 ba.

Coronavirus sabuwar cuta ce a duniya baki daya kuma ana cigaba da zurfafa bincike dan gano hanyoyin yimata rigakafi da maganinta baki daya. Hukumar magance cututtuka masu yaduwa ta Najeriya wato Nigerian Centre for Disease Control (NCDC) dama hukumar lafiya ta duniya wato World Health Organization (WHO) basu ayyana wani magani ba da za’ace yana warkar da cutar Coronavirus har yanzu. Abinda kawai akeyi shine, wadanda aka samu da cutar ana killace su tare da basu kulawa a likitance a wassu wurare da aka tanadi kayayyakin aiki na musamman dan ririta cutar har lokacin da kaifi ko zagayen rayuwar ita cutar zai kare, ana hakan ne dan kare mai dauke da cutar daga illar da zata iya haifar masa.

Kamar yadda Mr. Martins Ekor, wani kwararre kuma masanin kimiyya sarrafa magani ya bayyana, ba gaskiya bane cewa magungunan gargajiya basu da illa ga lafiya, ya kara da cewa, akwai rudani mutane acikin wannan zance.

Mr. Ekor ya gayawa jaridarthe Tribune cewa “magungunan gargajiya suna haifar da illolin rashin lafiya da suke kara zama barazana ga lafiyar mutane wanda a wassu lokutan ma suna samar da rashin lafiya na din-din-din, ko masu barazana ga rayuwar ma dama wanda suke kisa”

Kawo lokacin hada wannan rahoto, Najeriya ta kara samun billar cutar Coroanvirus guda goma sha hudu (14) wannan shine ya daga yawan wanda suke dauke da kwayar cutar a Najeriya zuwa sittin da biyar, wannan shine yanayin da ake ciki kawo ranar Alhamis  26 ga Maris, 2020 da misalign karfe 8:35pm

Kamar yadda hukumar hana yaduwar cututtuka  NCDC ta bayyana, an samu billar cutar guda goma sha biyu (12) a jihar Lagos sannan guda (2) a Birnin Tarayya Abuja (FCT).

Acikin billar cutar guda goma sha hudu (14), shida (6) daga ciki an gano su ne daga jirgi, uku (3) matafiya ne da suka dawo, daya (1) kuma yayi alaka ta kusa ne da wani mai dauke da cutar.

Karkarewa

Jita-jitar da ake yadawa cewa in aka hada Lemon Tsami, Citta da Uda da Uziza aka dafa sannan aka shaki tururin zaiyi maganin cutar Coronavirus zance ne marar tushe dan binciken masana a fannin lafiya bai gano hakan ba. Hukumar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC da hukumar lafiya ta duniya WHO sun gargadi mutane dasu guji magani da kansu ko hanyar shan kwayoyi ko tan hanyar yin anfani da maganin gargajiya saboda hakan na iya zama babbar barazana ga lafiyar mutum koma yakai ga

 salwantar rai baki daya. Tantancewar Mu: Labari Ne Maras Tushe #AdenaYadaLabaranKarya

Leave a Comment

Your email address will not be published.