5G Bashi Da Alaka Da Cutar Coronavirus

Gaskiyar Magana: Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa wannan jita-jitar da ake yadawa cewa 5G yana haifar da Cutar Corona labari ne na Bogi!

Tushen Magana: adaidai lokacin Cutar Corona ke cigaba da yaduwa, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bukasa Demokaradiyya da Cigaba wato Centre for Democracy and Development (CDD) suna cigaba da aikin su na bin diddigin labaran karya dan gano tushen su ba-dare-ba-rana.

Misali, daya daga cikin wadannan labarai marasa tushe shine wani kirkirarren batu da ya janyo cece-kuce da muhawara, wannan batu ba wani bane face “maganar da ake tafka muhawara akanta cewa akwai alaka tsakanin 5G (sabon tsarin saurin anfanin da yanar gizo) da kuma Cutra Corona ko COVID-19”.

Masu anfani da shafin sada zumunta Facebook a fadin duniya suna ta wallafawa tare da yayata maganganu cewa wannan tsari na saurin anfani da yanar gizo na 5G shine ke sa mutane kamuwa da cuta amma ba Cutar Corona ko COVID-19, kuma mutane da dama sun mutu sakamakon illar da tsari na 5G ke haifarwa.

A Najeriya, tsohon Sanata mai wakiltan jihar Kogi Ta Tsakiya,  Dino Melaye yayi zargin cewa bincike ya nuna Cutar Corona ba ita bace kalubalen da duniya ke fuskanta ahalin yanzu. Melaye a wata magana da wallafa a ranar Asabat  4 ga watan Afirilun, 2020, yace, daga binciken da ya gudanar, Cutar Corona ba ita bace matsala ba a yanzu. Babbar matsalar itace wannan tsarin na 5G da ake ta jinkirin gabatar dashi.

Sanatan ya fitadda maganganu dan kara tabbatar da zargin sa da suka hada da bada jawabi ga yan jaridu inda yace kanfanin MTN Nigeria sun sanar da gwaji da zasuyi na wannan tsari na 5G a Najeriya.

Har yanzu dai akan batun 5G din, tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama Femi Fani-Kayode da Shugaban Majami’ar Christ Embassy, Fasto Chris suma sun jaddada jita-jita. Fani Kayode da Fasto Chris sun alakanta Cutar Corona da 5G inda sukace wannan wata makarkashiya ce ta gabatar mulkin mallaka na kasashe masu karfi.

Har wayau, daga 23 ga watan Maris zuwa 4 ga watan Afirilun 2020, akwai muryoyi da dama da aka nada kuma aka yada ta manhajar WhatsApp da sauran kafafen sadarwa ana yada wannan magana marras tushe.

Gaskiyar Magana: 5G baya kawo Cutar COVID-19. Akwai nau’i guda biyu da 5G yake dasu. Na farko shine “sub-6 GHZ” wanda nisan zangon sa yana kasa da ma’auni na 6 GHz. Na biyun shine “millimeter wave” shi kuma nisan zangon sa ya wuce ma’aunin “24 GHz”. Su sunadaran sub-6 GHz bawai kwata-kwata basu da alaka da 5G da 4G bane. Wi-fi da microwaves suna aiki ne da sinadarin sub-6 GHz.

Masu manufar jirkita fahimtar mutane game da 5G sunyi anfani da kaddamarwa da kuma gano wannan tsari a kasar China a matsayin hujjar su. Amma 5G din kasar China yayi anfani ne da sub-6 GHz. Haka huma microwave din muke anfanin dashi anan bai haifar mana da Cutar Corona ba a duk tsawon shekarun da mu dauka muna anfani dashi, saboda haka 5G bazai haifar mana da Cutar Corona ba. Hasali ma, bai kamata muyi tunanin fuskantar rashin lafiya ba sakamakon anfani da 5G.

A wani jawabin da ta fitar a shafinta na yanar gizo akan wannan batu, hukumar lafiya ta majalisar dinkin duniya WHO tace: “bayan gudanar da baincike mai zurfi, kawo yanzu babu wata matsananciyar rashin lafiya da mu’amala da na’urori da za’a iya sarrafa su ba tare da kulla waya ba” zasu haifar. WHO ta kara da cewa zata cigaba da nazarin bincike-binciken da ake gudanarwa a wannan bangaren kuma zata wallafa sakamako dangane da batutuwan lafiya da suka shafi zangon sadarwa na waya a shekata 2022.

Hukumar lafiyar ta duniya ta kara da cewa abinda yake samar da hulda tsakanin jikin dan’adam da zangon sadarwa shine dumama da ka’iya faruwa. Hakanan hukumar lafiyar ta cigaba da cewa yadda ake ta’ammuli da na’urori a yanzu baya haifar da wani yanayi da ka’iya zama matsala ga jikin dan’adam.

WHO tace babu wata barazana ga lafiyar al’umma indai har ta’ammulin yana kan ma’auni mafi karanci da kuma sharudan kasa da kasa.

Game da Cutar COVID-19, WHO da hukumar dakile cutuka ta Najeriya NCDC sunyi ittifakin cewa cutar ta samo asali ne daga dabbobi kafin yaduwar ta zuwa dan’adam.

A wani martani da ya mayar cikin gaggawa, Ministan Ma’aikatar Sadarwa da Tattalin Arziki Ta Fannin Sadarwa, Dr. Isah Ali Ibrahim Pantami ta cikin takarda da aka rabawa manema labarai a ranar 4 ga watan Afirilu shekara ta 2020, yace ba’a bada lasisi ko umarnin kaddamar da tsarin 5G a Najeriya ba. Dr. Pantami ya cigaba da cewa an bada izinin gwajin tsarin na 5G na tsawon watanni uku kuma gwajin ya fara aiki tun ranar 25 ga watan Nuwanba shekara ta 2019, kuma anyi hakanne dan gano cewa ko tsarin yana da illa ga lafiya ko al’amarin tsaro a Najeriya.

Minista Pantami yace: “a matsayin gwaji, na umarci ma’aikatar kula da harkokin sadarwa wato Nigeria Communications Commission (NCC) da su tabbatar da cewa ayarin kwararru, masana tsaro da dai sauran masu ruwa-da-tsaki sun shiga cikin wannan lamari na gwaji, hakanan ofishina ya gayyaci duk wadanna hukumomi na gwamnati dan suma su shaida yadda wannan gwaji zai kasance, ahalin yanzu, gwajin ya kankama, ana cigaba da yin nazari akan sakamakon gwajin kuma ana cigaba da rubuta rahoton”.

Kammalawa:

Babu wani sahihin bincike da ya tabbatar da alaka tsakanin samar da 5G da annobar Cutar Corona ko COVID-19. Hakanan kuma babu kanfanin sadarwa a Najeriya da yake gabatar da ayyukan akan tsarin 5G saboda har yanzu gwamnati bata bada umarnin yin hakan ba. CDD tana jan hankalin mutane da su guji daukar farfagandar da wassu sanannun mutane ke yadawa akan wannan al’amari.

Leave a Comment

Your email address will not be published.